Isa ga babban shafi

Shugabannin Afrika sun fusata da yadda takwarorinsu na Turai suka kauracewa taron yanayi

Shugabannin kasashen Afirka sun bayyana takaici a game da yadda takwarorinsu na kasashen yammacin Duniya, saboda yadda suka kaurace wa taron birnin Rotterdam da ke kokarin samar da kudaden da za a yi amfani da su don yaki da matsalolin sauyin yanayi a nahiyar Afirka.

Shugaban Tarayyar Afrika, Sénégal Macky Sall.
Shugaban Tarayyar Afrika, Sénégal Macky Sall. AP - JOHN ANGELILLO
Talla

Shugaban Senegal Macky Sall da ke rike da shugabancin Tarayyar Afirka da takwaransa na Congo Felix Tshisekedi sun ce ko ba komai, manyan kasashe a matsayinsu na wadanda ke da alhakin gurbata muhalli ya kamata su kasance a wurin wannan taro.

Shugabannin biyu dai na jawabi ne a wajen taron birnin Rotterdam na kasar Netherlands wanda a lokacinsa ne ya kamata a rattaba hannu kan daftarin yarjejeniyar da za gabatar wa taro COP27 dangane da dumamar yanayi da zai gudana cikin watan nuwamba mai zuwa a kasar Masar.

Macky Sall ya bayyana rashin kasancewar shugabannin manyan kasashe a wannan taro a matsayin abin takaici, ya na mai jaddada cewa wadannan kasashen ne suka haifar da sauyin yanayi, saboda haka ya kamata a koda yaushe ake tattauna batu ya kamata su kasance a halarce.

Daga farkon wannan taro har zuwa yanzu, Firaministan Netherlands Mark Rutte mai maukin baki kawai ne ya kasance a zauren taron, abin da shugaban Congo Tshisekedi ya ce sam bai wadatar ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.