Isa ga babban shafi

Taron yanayi na Kenya ya nemi Duniya ta ceto halittun da ke shirin gushewa

Wakilan da ke shiga tsakani daga majalisar dinkin duniya a taron sauyin yanayi sun bukaci kasashen duniya da su ware kaso 30 cikin dari na fadin kasar su da nufin alkinta sauran hallitu da ke doron duniya.

Wasu giwaye a dajin Kenya.
Wasu giwaye a dajin Kenya. © RFI/Victor Moturi
Talla

Taron na birinin Nairobi na mayar da hankali ne game da shawo kan sauyin yanayi, yayinda duniya ke fama da dumamar  yanayi mafi muni a tarihi.

Tuni dai masana kimiyya suka ce akalla na’uin hallitu miliyan daya ne ke cikin hadarin karewa a duniya, sakamakon gurbacewar yanayin da zasu iya rayuwa a cikin sa, dalili kenan da wakilan majalisar dinkin duniya a taron ke ganin ya kamata kasashen duniya su farga.

A cewar Masanan, ware kaso 30 cikin dari na fadin kowacce kasa da killace shi don amfanin manyan namun daji, tsirrai da sauran hallitu zai taimaka ainun wajen dai-daita yanayi da kuma baiwa sauran hallitun da ke barzanar karewa damar ci gaba da yaduwa.

Ko da yake karin haske kan tsarin da aka yiwa take da 30 by 30 wato dai ware kaso 30 na fadin kasa kafin shekarar 2030, ministan muhalli na China Huang Runqui ya ce yana da kwarin gwiwar matukar kasashe suka rungumi wannan shiri zai taimaka a yakin da ake yi da sauyin yanayi cikin sauki.

Masana kimiyya sun yi ammana cewa na’uin hallitu da suka hada da tsirrai, kwari da kuma dabbobi na ruwa da na tsandauri sama da miliyan 10 ne ke mutuwa kowacce shekara sakamakon rashin yanayi mai kyau da zasu iya rayuwa, wanda kuma dan adam ne ke da alhakin hakan ta hanyar kona dazuka, da kuma lalata muhalli ta hanyoyi daban-daban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.