Isa ga babban shafi

Dole kasashen Afirka su lalubo hanyar ceto yanayi da kawar da talauci - Buhari

A yayin da aka bude taron kungiyar ministocin kasashen Afrika da ke kungiyar kare muhalli ta Pan African Great Green Wall a Abuja, shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya ce dole ne kasashen Afrika su ci gaba da lalubar hanyoyi dabam dabam na yakar canjin yanayi, kwararowar hamada, yunwa da fatara a nahiyar.

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari.
Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari. AFP - LUDOVIC MARIN
Talla

Shugaba Buhari ya ce yunkurin kare muhalli na daya daga cikin dalilan da suka sa Najeriya ta kaddamar da shirin kawar da hayaki mai gurbata muhalli a shekarar 2060, yayin da take mayar da hankali a kan yadda za ta habaka hanyoyin samun makamashi mai tsafta tare da bunkasa noma da masana’antu.

Shugaba Buhari, wanda mataimakinsa Farfesa Yemi Osinbajo, ya wakilta a taro ministocin kasashen Afrika da ke cikin wannan kungiya ta kare yanayi da yaki da yunwa da fatara na 8 da aka bude a Abuja, ya ce wajibi ne a yi amfani da damammakin da ake samu a taruka irin wannan wajen tunatar da juna a kan shirin ceto yanayi.

Bayan da ya bude taron ne, mataimakin shugaban Najeriya ya kaddamar da gangamin dashen itatuwa, yana mai kira ga sauran jihohin kasar su bi sahu don kasar ta cika alkawarinta na dasa itatuwa miliyan 25 a cikin shekaru 2.

Najeriya na cikin wannan kungiya, wadda makasudin kafa ta shine maido da muhallin nahiyar Afrika da ya gurbace cikin hayyacinsa, tare da inganta rayuwar miliyoyin al’ummarta, a yayin da take habaka samar da abinci da kuma inganta yanayi.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.