Isa ga babban shafi

Mutane fiye da 400 sun mutu, sama da dubu 3 sun jikkata a rikicin Sudan

Majalisar Dinkin Duniya ta ce mutane sama da 400 suka mutu ya zuwa wannan lokaci a rikicin kasar Sudan, yayin da sama da 3,500 suka samu raunuka daban daban. 

Yadda aka ragargaza wasu gine-ginen fararen hula a rikicin kasar Sudan. 20 ga Afrilu, 2023.
Yadda aka ragargaza wasu gine-ginen fararen hula a rikicin kasar Sudan. 20 ga Afrilu, 2023. AP - Marwan Ali
Talla

Majalisar ta kuma kara da cewa daga cikin mutanen da suka mutu akwai yara kanana guda 9, bayan sama da 50 da suka jikkata. 

Mai Magana da yawun hukumar lafiya ta duniya Margareth Harris ce ta gabatar da wadannan alkaluma masu tada hankali, sakamakon rahotannin da suke tattarawa daga hannun hukumomin lafiyar Sudan. 

Harris ta ce yanzu haka asibitocin kula da lafiyar jama’a guda 20 sun daina aiki a Sudan saboda tashin hankalin, yayin da wasukarin 12 ke fuskantar barazanar dakatar da aikace aikacensu, wanda ake ganin na iya haifar da karin illa ga jama’a. 

Shima mai Magana da yawun Hukumar da ke kula da kananan yara ta Majalisar wato UNICEF, James Elder ya ce rufe asibitocin ba wai kawai zai shafi wadanda suka samu raunuka sakamakon wannan tashin hankalin bane, har ma da marasa lafiyar da ke bukatar kulawa. 

Elder ya ce dama kasar Sudan na daya daga cikin kasashen da ke da yawan yara masu fama da tamowa, kuma ganin yadda wannan rikici yayi kamari, ana iya samun karin yara kusan dubu 50 da za su fuskanci wannan matsala. 

Wasu 'yan Sudan yayin halartar Sallar Eid al-Firtr a Khartoum babban birnin kasar. Juma'a, 21 ga Afrilu, 2023.
Wasu 'yan Sudan yayin halartar Sallar Eid al-Firtr a Khartoum babban birnin kasar. Juma'a, 21 ga Afrilu, 2023. AP - Marwan Ali

Rahotanni sun ce har a yau da juma’a ke bikin Sallar Idi, ana ta yin barín wuta tsakanin bangarorin biyu da ke kokawar mulki a cikin kasar. 

Kungiyar likitoci ta kasa ta ce daren jiya anyi ta jin karar fashewar bama bamai da kuma amon makaman atilare a birnin Khartoum, yayin da sojojin gwamnati da na kungiyar RSF ke musayar wuta da bindigogi a tsakaninsu. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres tare da Sakataren harkokin wajen Amurka Antony Blinken sun bukaci tsagaita wuta nan tsawon kwanaki 3 domin bai wa jama’a damar gudanar da bukukuwan Sallah. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.