Duk da yarjejeniyar tsagaita wuta an ci gaba da luguden wuta a Sudan
Ana ci gaba da luguden wuta a birnin Khartoum na kasar Sudan bayan da sojojin kasar suka ayyana tsagaita bude wuta na tsawon kwanaki uku, kuma ba a san tushen harbe-harben ba, kamar kamfanin dillancin labarai na Reuters ya tabbatar.
Wallafawa ranar:
Haka zalika ana ci gaba da jiyo amon harbe-harbe da kuma fashewar nakiya a wasu wurare.
Rundunar sojin Sudan ta ce ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta tsawon kwanaki uku, domin baiwa al'ummar Sudan damar gudanar da bukukuwan karamar Sallah, bayan kawo karshen azumin watan Ramadan.
Sanarwar da rundunar ta fitar ta ce dakarun sojin kasar na fatan 'yan tawayen za su bi dukkan sharuddan tsagaita bude wuta da kuma dakatar da duk wani yunkuri na soji da zai kawo mata cikas.
A ranar Juma'a ne dakarun kai daukin gaggawa na musamman suka fara fafatawa da sojoji a fadin kasar Sudan kusan mako guda.
Ko da yake rundunar da ke biyayya ga mataimakin shugaban gwamnatin mulkin sojin kasar, Janar Mohammed Hamdan Dagalo ta amince da yarjejeniyar tsagaita wutar ta tsawon sa’o’I 72.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu