Isa ga babban shafi

Kasashen duniya na rige-rigen kwashe mutanen su daga Sudan

Yakin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada tsakanin dakarun Sudan biyu, manyan kasashen duniya na rige-rigen kwashe ‘yan kasashen waje ta hanyoyi daban-daban da suka hada da mota da ruwa da kuma jiragen sama.

Yakin da ake gwabzawa tsakanin dakarun Sudan biyu ya tilastawa manyan kasashen duniya rige-rigen kwashe ‘yan kasashen waje ta hanyoyin mota da ruwa da kuma jiragen sama.
Yakin da ake gwabzawa tsakanin dakarun Sudan biyu ya tilastawa manyan kasashen duniya rige-rigen kwashe ‘yan kasashen waje ta hanyoyin mota da ruwa da kuma jiragen sama. AFP - ABUBAKARR JALLOH
Talla

A yayin da kazamin fada da ake gwabzawa tsakanin dakaru da ke biyayya ga manyan janar-janar biyu na Sudan, kasashe da dama sun sanar da kwashe ‘yan kasarsu da wasu baki daga Khartum babban birnin Sudan.

Yawancin kasashe na amfani da birnin Port Sudan dake gabatar tekun Bahar Maliya, mai tazarar kilomita 850 daga birnin Khartoum wajen kwashe baki daga kasar.

Filin jiragen saman Khartoum

Saboda babban filin tashi da saukar jiragen sama na Khartoum babban birnin kasar ya kasance filin daga tsakanin bangarorin sojin biyu da basa ga maciji da juna, kuma filin na karkashin ikon dakarun Rapid Support Forces (RSF) dake fafatawa da gwamnati.

Ga abin da kasashe daban-daban ke yi a kokarin kwashe 'yan kasar su da suka makale zuwa tudun mun tsira.

-Saudiya-

Kasar Saudiyya ce ta jagoranci kwashe kason farko na baki cikin nasara, inda ta kwashe sama da mutane 150 da suka hada da jami'an diflomasiyya ta Port Sudan a ranar Asabar.

Yadda Sudiya ta kwashe baki daga Sudan, 22/04/23
Yadda Sudiya ta kwashe baki daga Sudan, 22/04/23 via REUTERS - SAUDI PRESS AGENCY

Saudiya tace 'yan kasar ta 91 da na wasu 66 daga wasu kasashe 12 da suka hada da Kuwait da Qatar da Hadaddiyar Daular Larabawa da Masar da Tunisia da Pakistan da Indiya da Bulgaria da Bangladesh da Philipines da Canada da Burkina Faso sun isa gida lafiya.

sauran kasashe

Amurka ma ta sanar da kwashe sama da mutane 100 a wannan lahadi ta wasu jiragen sojinta masu saukar angulu uku.

Faransa m ata sanar da kwashe sama da mutane 100, yayin da Sojojin Burtaniya suka kwashe ma'aikatan ofishin jakadancin kasar da iyalansu.

Yadda dakarun Faransa suka kwashe wasu 'yan kasar daga Sudan,23/04/23
Yadda dakarun Faransa suka kwashe wasu 'yan kasar daga Sudan,23/04/23 © État major des armées / AFP

Sauran kasashe da suka sanar da nasarar kwashe ‘yan kasarsu da karin wasu baki, sun hada da Turkiya da Spain da Jamus da kuma Netheland.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.