Isa ga babban shafi

Sama da mutane 150 da aka kwashe daga Sudan sun isa Saudiyya

Fadan da ake gwabzawa a Sudan ya shiga mako na 2 a yayin da kasashe suka samu damar fara kwashe mutannesu daga kasar, inda rikici ya barke tsakanin sojin kasar da rundunar kai daukin gaggawa ta musamman a makon da ya gabata.

Ana ci gaba da gwabza fada a maako na biyu kenan a Sudan.
Ana ci gaba da gwabza fada a maako na biyu kenan a Sudan. © INSTAGRAM @LOSTSHMI via REUTERS
Talla

Sama da mutane150 daga kasashe dabam dabam ne aka kwashe zuwa kasar Saudiyya a jiya Asabar a karon farko da aka fara kwashe fararen hula, biyo bayan tsagaita wuta na dan gajeren lokaci.

Kasashen waje sun ce suna shirin kwashe Karin dubban mutanensu zuwa tudun mun tsira duk kuwa da cewa babban filin jirgin saman Sudan yana a rufe.

Shugaban mulkin sojin kasar, Janar Abdel Fattah Burhan  ya sha alwashin taimakawa wajen wajen ganin an kwashe ‘yan kasashen Amurka, Birtaniya, China da Faransa bayan da ya gana da shugabannin kasashe da dama da suka nemi taimako.

Ficewa daga babban birnin kasar yana da matukar wahala, ganin cewa aksarin filayen jiragen sama sun koma filin daga.

Rikicin ya yi sanadin mutuwar daruruwan mutane tare da jikkata da dama, a yayin da ake fama da matsalar karancin wutar lantarki da abinci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.