An cigaba da barin wuta a Sudan duk da tsagaita wutar kwanaki 3
Rahotanni daga Sudan na cewa an jiyo amon harbe-harbe da manyan bindigogi a Khartoum da kuma Omdurman birni na biyu mafi girma a kasar.
Wallafawa ranar:
Sabon fadan ya barke ne duk da sabuwar yarjejeniyar tsagaita bude wuta ta tsawon sa'o'i 72 da Amurka jagoranci kullawa tsakanin sojojin Sudan da dakarun musamman na kai daukin gaggawa RSF, masu biyayya ga mataimakin shugaban Sudan Muhammed Hamdan Daglo.
A birnin Geneina da ke yammacin yankin Darfur, ma wani fadan ne ya barke a Talatar nan kamar yadda sahihan majiyoyi daga Sudan din suka bayyana.
Tuni Majalisar Dinkin Duniya ta sanar da dakatar da ayyukan jin kai a wasu sassan kasar, saboda kazancewar da rikicin kasar ke yi, wanda ya barke tun a ranar 15 ga watan nan na Afrilu.
Akalla mutane 427 aka tabbatar da mutuwarsu a rikicin na Sudan, yayin da wasu kusan dubu 4 suka jikkata.
Kawo yanzu kuma dubun dubatar baki ‘yan kasashen ketare da ma ‘yan kasar ta Sudan aka kwashe daga kasar zuwa kasashen Masar, Sudan ta Kudu da kuma Chadi cikin ‘yan kwanakin da suka gabata.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu