Isa ga babban shafi

Air Peace ya yi tayin kwaso 'yan Najeriya da ke Sudan kyauta

Kamfanin sufurin jirgin saman Air Peace ya yi tayin bayar da gudumawar kwaso daliban Najeriya da suka makale a Sudan kyauta. 

Wasu daga cikin jiragen kamfanin Airpeace da ke Najeriya.
Wasu daga cikin jiragen kamfanin Airpeace da ke Najeriya. © Airpeace
Talla

 

Da ya ke tayin na kamfanin, Shugabansa Allen Onyeama ya ce dalibai da sauran ‘yan Najeriya da suka makale a Sudan din na bukatar daukin gaggawa, kuma a yanzu ba lokaci ne da za’a zauna jan kafa ba. 

A cewar sa abinda yake bukata kadai, shi ne ‘yan Najeriya da ke Sudan su yi kokarin fita daga kasar zuwa wata kasa makwaciyar Sudan, jirgin Kamfanin kuwa zai je ya kwaso su ba tare da bata lokaci ba, kasancewar Sudan ta kulle dukannin sararin samaniyar ta. 

Idan dai mai sauraro zai iya tunawa, tuni ministan harkokin wajen Najeriya Geoffrey Onyeama ya ce Najeriya ta shirya tsaf don fara kwaso al’ummar ta daga Sudan din. 

Fiye da ‘yan Najeriya dubu biyar ne yanzu haka ke makale a Sudan, wadanda mafi yawan su mata ne musamman a birnin Khartoum, inda barin wuta ya fi muni, kuma kawo yanzu suna ta kiraye-kiraye ga gwamnati da ta kawo musu daukin gaggawa. 

Wannnan dai ba shi ne karon farko da kamfanin Air Peace ke irin wannan aiki na kwaso ‘yan Najeriya a kasashen da suke fama da rikici ba, don kuwa ko a shekarar 2019 sai da ya kwaso ‘yan Najeriya da suka makale a Africa ta Kudu bayan barkewar rikicin wariyar launin fata.   

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.