Muhammad Bashir kan halin da daliban Najeriya ke ciki a Sudan
Wallafawa ranar:
Kunna - 03:41
Dalibai ‘yan Najeriya da ke makale a Sudan na ci gaba da kiraye-kirayen a yi gaggawar kwashe su daga kasar mai fama da rikici, wanda ya barke yau fiye da mako guda. Rahotanni sun ce a halin da ake ciki, fada tsakanin dakaru masu biyayya ga babban hafsan sojin Sudan, Abdel Fattah al-Burhan, da wadanda ke goyon bayan mataimakinsa, Mohamed Hamdan Daglo ya rutsa da kimanin daliban Najeriyar dubu 4000.
Kan wannan batu ne Nura Ado Suleiman ya tattauna da shugaban kungiyar daliban Najeriya da ke karatu a kasashen ketare Muhammad Bashir.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu