Isa ga babban shafi

Sama da mutum 14,000 ne suka tsere zuwa Habasha daga Sudan - MDD

Majalisar dinkin duniya ta ce fiye da mutane 3,500 ne suka tsere daga Sudan kawo yanzu kuma suke samun mafaka a Etofia, yayin da sama da 14,000 suke gudun hijira a masar. 

Jirgin saman sojin kasar Faransa kenan, lokacin da yake kwashe 'yan kasar daga Sudan.
Jirgin saman sojin kasar Faransa kenan, lokacin da yake kwashe 'yan kasar daga Sudan. via REUTERS - FRENCH PRESIDENT EMMANUEL MACRON
Talla

Hukumar kula da ‘yan gudun hijirar Majalisar dinkin duniyar ce ta tabbatar da hakan ga kamfanin dillancin labaran Faransa AFP. 

Hukumar ta ce akwai fargabar adadin ka iya zartawa zuwa dubu 270,000 inda wannan adadi zasu nemi mafaka a kasashen Itofiya, Chadi da Egypt. 

A cewar hukumar cikin wadanda suka tsere daga Sudan din yanzu haka har da wadanda ba ‘yan asalin kasar ba, musamman ‘yan Turkiyya da kuma mutanen Habasha, yayin da ta kara adadin sansanonin gudun hijirar da take da su a akan iyakokin makwarftan kasashen Sudan din daga 200 zuwa 1,300 cikin makon da ya gabata kadai.  

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.