Isa ga babban shafi

Ana ganin gawarwaki warwatse a titunan Sudan yayin da mutane ke tsarewa rikici

Rahotanni daga kasar Sudan na cewa Dubban mutane na tsarewa Khartum babban birnin kasar, inda shaidun gani da ido suka ce ana ganin gawarwakin mutane warwatse a kan tituna, yayin da ofisoshin jakadanci suka ce sama da fararen hula 270 ne aka kashe a fadan da ake gwabzawa tsakanin sojoji da dakarun sa kai na RSF

Khartoum babban birnin Sudan, 19/04/2023
Khartoum babban birnin Sudan, 19/04/2023 AP - Marwan Ali
Talla

Bayanai suka ce Dubban mutane na tserewa daga Khartoum babban birnin kasar ne domin gujewa fadan da ake cigaba da gabzawa tsakanin sojojin kasar masu biyayya ga shugaba Abdel Fattah al Burhan da kuma dakadarun rundunar sakai na RSF masu biyayya ga mataimakin shugaban Muhd Hamdan Daglo.

 Kazamin fadan dai ya shiga rana ta shida da barkewa ne bayan da bangarorin masu rikici da juna suka bijirewa yarjejeniyar tsagaita wutar wucin gadin da aka kulla. 

Sama da mutum 270 suka mutu

Ofisoshin jakadancin kasashe dake birnin Khartoum sun ce, fadan da ake cigaba da gwabzawa ya yi sanadin mutuwar mutane fiye da 270 zuwa daren Laraba, wato cikin kwanaki biyar bayan barkewar tashin hankalin a ranar Asabar. 

Sai dai akwai fargabar adadin mamatan ka iya zarce wanda hukumomin suka bayyana, la’akari da cewar akwai dimbin mutanen da suka jikkata da har yanzu suka gaza zuwa asibiti domin samun kulawa, yayin da shaidun gani da ido suka ana ganin gawarwaki yashe a kan tituna.

Fyade

Bayanai sun ce an kaiwa jami’an diflomasiya hare-hare, yayin da shugaban hukumar kula da ayyukan jin kai ta majalisar dinkin duniya Martin Griffiths ya ce sun samu  rahotannin cin zarafi harma da fyade da aka yi  wa wasu jami’an agaji a kasar ta Sudan. 

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Antonio Guterres ya sanar da cewa zai gana da shugabannin kungiyar Tarayyar Afirka da kungiyar hadin kan Larabawa kan rikicin na Sudan, kamar yadda kakakinsa ya shaida wa manema labarai.

Sojojin Masar

A halin da ake ciki Rundunar sojin Sudan ta ce na kwashe sojojin Masar 177 da RSF ta kama a garin Merowe da ke arewacin kasar, zuwa gida cikin jiragen sama guda hudu na jigilar sojojin Masar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.