Isa ga babban shafi

Sabon rikici ya barke a yankin Darfur na Sudan

Sojojin Sudan sun yi luguden wuta ta sama a birnin Khartoum babban birnin kasar, yayin da ake ci gaba da gwabza kazamin fada a yankin Darfur kwanaki 13 kenan da fara rikicin kasar duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta.

Wani jirgin ruwa dauke da fararen hula 1,687 daga kasashe sama da 50 da ke gudun hijira a Sudan, ya isa sansanin sojojin ruwa na Sarki Faisal da ke Jeddah a ranar 26 ga Afrilu, 2023.
Wani jirgin ruwa dauke da fararen hula 1,687 daga kasashe sama da 50 da ke gudun hijira a Sudan, ya isa sansanin sojojin ruwa na Sarki Faisal da ke Jeddah a ranar 26 ga Afrilu, 2023. AFP - AMER HILABI
Talla

Da yammacin ranar Laraba, rundunar sojin kasar ta ce ta amince da tattaunawa a Juba, babban birnin makwabciyar kasar wato Sudan ta Kudu, kan tsawaita wa'adin tsagaita bude wuta na kwanaki uku da zai kare a ranar Juma'a, bisa shawarar kungiyar IGAD ta kasashen yankin gabashin Afirka.

An dai yi kokarin sasanta bangarorin biyu tun bayan fadan da ya barke a ranar 15 ga watan Afrilu tsakanin sojojin Sudan karkashin jagorancin Janar Abdel Fattah al-Burhan da kuma dakarun Rapid Support Forces (RSF) karkashin jagorancin mataimakinsa Mohamed Hamdan Daglo.

An dai ci gaba da gwabza fadan duk da yarjejeniyar tsagaita bude wuta a ranar Talata, inda jiragen yaki suka yi ta sintiri a sararin samaniyar yankunan arewacin babban birnin kasar, yayin da mayakan da ke kasa suka yi ta musayar wuta da manyan bindigogi.

Rundunar sojin kasar ta ce, Burhan ya amince da kudirin kungiyar IGAD na zaman tattaunawa kan tsawaita tsagaita bude wuta da karin sa'o'i 72.

Rahotanni daga kasar sun tabbatar da cewa, tsohon shugaban kasar, Omar El-Bashir dama na karbar kulawar likitoci a asibiti, tun kafin rikicin ya barke. asibiti kafin a fara fada.

Akalla mutane 512 ne suka mutu yayin da wasu 4,193 suka jikkata a fadan, a cewar alkaluman ma’aikatar lafiya, ko da yake adadin wadanda suka mutu na iya karuwa sosai.

Bayan babban birnin kasar, fada ya barke a larduna, musamman a yankin Darfur da ke yammacin kasar da yaki ya daidaita.

Wannan kazamin fadan ya dabaibaye fararen hula da dama a gidajensu, inda suke fama da karancin abinci, ruwan sha da wutar lantarki.

Majalisar Dinkin Duniya ta yi gargadin cewa mutane kusan 270,000 za su iya tserewa zuwa kasashen Sudan ta Kudu da Chadi da ke makwabtaka da kasar.

Wasu daga cikin 'yan Sudan din da suka tserewa yakin, sun nemi mafaka a Masar daga arewaci, inda daga Gabashin kasar kuma, wasu sun nemi mafaka ne a Habasha, kuma dukkanin su sun yi doguwar tafiya ne da kafa kafin su isa kasashen.

A yayin da ake fama da rashin bin doka da oda a Sudan, an tafka ta’asa a gidajen yari da dama, ciki har da na babban gidan yarin Kober inda ake tsare da manyan mukarraban hambararren shugaban kasar Omar al-Bashir.

Daga cikin wadanda suka tsere daga gidan yarin, akwai Ahmed Haroun, wanda kotun hukunta manyan laifuka ta kasa da kasa ke nema ruwa a jallo bisa laifukan yaki da cin zarafin bil adama, saboda rawar da ya taka a rikicin yankin Darfur da ya barke shekaru ashirin da suka gabata.

Tserewar da Haroun ya yi ya haifar da fargabar shigar masu biyayya ga Bashir a cikin fadan da ake ci gaba da yi.

Sai dai rundunar sojin kasar ta tabbatar da cewa hambararren shugaban kasar ba ya cikin wadanda suka tsere amma an kai shi asibitin sojoji kafin fadan ya barke.

Sojoji sun hambarar da El-Bashir a wani juyin mulki a cikin watan Afrilun 2019 bayan zanga-zangar da ta haifar da fatan shirin mika mulki ga farar hula.

Janar-janar din guda biyu sun yi juyin mulki tare a shekara ta 2021, na baya-bayan nan shine, kan shirin shigar da rundunar RSF cikin rundunar soja ta kasar Sudan din.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.