Isa ga babban shafi

An sake tsagaita wuta a rikicin Sudan

Rundunar Sojin Sudan da Dakarun kai Daukin Gaggawa na RSF da ke rikici da juna sun sake amincewa da tsagaita wuta da karin tsawon wasu awanni 72. 

À gauche, le chef des forces armées soudanaises, le général al-Burhan et à droite celui des Forces de soutien rapide, le général Hemedti.
À gauche, le chef des forces armées soudanaises, le général al-Burhan et à droite celui des Forces de soutien rapide, le général Hemedti. AFP - ASHRAF SHAZLY
Talla

A jawabin da ya gabatar ranar asabar game da rikicin,  Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya, Antyonio Guterres ya ce babu amfanin ci gaba da yaki a kan mulkin kasar da ke neman rugujewa, kuma wannan na zuwa ne a yayin da aka shiga mako na 3 da soma rikici tsakanin rundunar sojin Sudan da dakarun Kai Daukin Gaggawa na RSF. 

Duk da cewa bangarorin biyu sun sake amincewa da yarjejeniyar tsagaita wuta na karin kwanaki 3, jaridu sun bayyana irin ta’adin da suka yi wa juna. 

Tuni dai rundunar ‘yan sandan Sudan ta aike da wasu daga cikin jami’anta babban birnin Khartoum domin tabbatar da tsaro. 

Hukumar Abinci ta Duniya ta koka tare da yin gargadin cewa fadan da ake ci gaba da gwabzawa a halin yanzu ka iya jefa yankin gabashin Afrika cikin wani rikici na jinkai. 

Rikicin na Sudan dai ya mayar da Khartoum tamkar filin daga, sannan ya jefa illahirin kasar cikin halin kaka-ni-kayi, ya kuma tilasta wa dubbai tserewa zuwa wasu kasashe da ke makotaka da kasar, yayin da ya yi sanadiyar mutuwar sama da mutane 500. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.