Isa ga babban shafi

Pakistan ce ta 3 a jerin kasashe mafiya gurbatacciyar iska

Binciken da wani kamfanin kasar Switzerland mai samar da na’urorin tace iska ya gudanar, ya nuna cewa Lahore na kasar Pakistan ne birnin da aka fi samun iska mafi gurbata a duniya a shekarar 2022. 

Bayan Pakistan kasashen da ke fama da wannan matsala da gurbacewar iska akwai India da Bangladesh kana Chadi a Afrika.
Bayan Pakistan kasashen da ke fama da wannan matsala da gurbacewar iska akwai India da Bangladesh kana Chadi a Afrika. AP - Altaf Qadri
Talla

Rahoton da kamfanin IQAir ya wallafa a Talatar nan ya ce, Pakistan ce kasa ta 3 daga cikin kasashe mafiya gurbatacciyar iska a duniya, a yayin da Bangladesh ke ta 5, India kuma ta 8. 

IQAir ya gwada ingancin iskar ne bisa la’akari da  burbushin wani sinadari mai illata huhu da ke bin iska, wanda ake kira PM2.5. 

Masu bincike, gwamnatoci, hukumomi da kungiyoyi na yawan amfani da alkalumman binciken wannan kamfani saboda ingancinsa. 

Iskar birnin Lahore ta gurbace da kashi 97 da digo 4 na burbushin sunadarin PM2.5  a ma’aunin micrograms, daga kashi 86 da rabi a shekarar 2021, abin da ya maida shi birni mafi gurbatacciyar iska a duniya. 

A yayin da kasar Chadi ta kai kashi 89.7 na wannan burbushin PM2.5, Iraqi, wadda ita ce kasa ta biyu mafi gurbatacciyar iska a duniya ta na da kashi 80 da digo 1. 

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta ce mutane miliyan 7 ne ke mutuwa duk shekara saboda matsalar tasirin gurbacewar iska. 

An shirya kundin na IQAir ne ta wajen amfani da bayanan da aka samu daga na’urar tantance ingancin iska har dubu 30 a sama da wurare dubu 7 dai 3 da ke kasashe da yankuna 131. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.