Isa ga babban shafi

Gurbatacciyar iska ta kashe yara 22,000 a jihar Legas dake Najeriya

Hukumomi a Najeriya sun ce sama da yara 22,500 ne suka mutu sakamakon gurbatacciyar a jihar Legas da ke kudancin kasar a 2021.

Adadin ya kai kashi 75 cikin 100 na mutane 30,000 da suka mutu
Adadin ya kai kashi 75 cikin 100 na mutane 30,000 da suka mutu AP - Altaf Qadri
Talla

Hukumar kare muhalli a jihar Legas din ta ce adadin ya kai kashi 75 cikin 100 na mutane 30,000 da suka mutu a shekarar 2021 a jihar saboda gurbacewar muhalli.

Shugabar Hukumar, Dolapo Fasawe, ce ta bayyana hakan ga manema labarai a wajen bikin kaddamar da shirin samar da iska mai kyawu, da aka gudanar a Legas.

Dolapo Fasawe ta ce an samu alkaluman ne daga wani rahoto da ke nuna yadda gurbacewar iska ke haifar da tarin matsaloli ga lafiyar mazauna jihar.

Ta ce a halin yanzu yankin Itedo na cikin yanayi mai ban tsoro game da gurbacewar muhalli, wanda ke bukatar daukar matakin gaggawa.

Hukumar kare muhallin dai ta ce ta yi nazarin ingancin iska kafin samar da shirin, bayan bincike ya gano cewa mutane da dama ba su san illar gurbacewar iska ga lafiya ba.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.