Isa ga babban shafi

Fasinjoji 16 sun bace sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Legas

Kwanaki 3 kacal bayan hatsarin jirgin ruwa da ya yi sanadin mutuwar mutane 2 a yankin Ikorodu dake Lagos a Najeriya, wani karamin jirgin ruwan ya sake yin hatsari a yankin Mile 2 a daren Juma’a, inda yanzu haka ake neman fasinjoji 16 da ke cikinsa.

Fasinjojin 16 sun bace sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Lagos, Najeriya.
Fasinjojin 16 sun bace sakamakon hatsarin jirgin ruwa a Lagos, Najeriya. © Premium Times
Talla

Shugabar hukumar kula da sufurin ruwa a jihar Lagos, Sarat Braimah ce ta tabbatar da aukuwar lamarin a wata sanarwa a jiya Asabar.

Braimah ta ce har yanzu ba a gano inda  ilahirin fasinjoji 16 da ke cikin jirgin ruwan suke ba.

Ta ce karamin  jirgin ruwan da ya tashi daga Mile 2 zuwa Ibeshe a yankin Ojo ya karya daya daga cikin ka’idojin hukumar  bayan da ya yi aiki cikin dare.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.