Isa ga babban shafi

Legas ya zama birnin na 2 mafi munin gudanar rayuwa a duniya - Rahoto

Wani rahoton masana tattalin arziki da suka saba fitarwa shekara-shekara da aka wallafa ana gaf da karkare makon nan, ya bayyana Legas dake Najeriya a matsayin birni na biyu mafi munin yanayin zamantakewa a duniya.

Wani yanki a birnin Legas dake kudancin Najeriya.
Wani yanki a birnin Legas dake kudancin Najeriya. PIUS UTOMI EKPEI / AFP
Talla

Birnin Damascus na kasar Syria da yaki ya daidaita kadai ne dai Legas yafi dadin zama a duniya, wanda a bana ma ya rike matsayinsa na zama mafi munin yanayin rayuwa a doron kasa.

A halin da ake ciki, Vienna babban birnin kasar Austria ne ya sake darewa matsayin birni mafi kyawun rayuwa a duniya.

A shekarar bana rahoton kwararrun bai hada da Kyiv babban birnin Ukraine ba, bayan da Rasha ta mamaye kasar a karshen watan Fabrairu.

Masana tattalin arzikin na nazartar batutuwa da dama da suka hada da wadatar ababen more rayuwa, ingancin sufuri, kiwon lafiya, ilimi da kuma tsaro da kwanciyar hankali wajen tantance matsayin yankuna ko biranen duniya dangane da kyawun zamantakewar da mutane ke yi a cikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.