Isa ga babban shafi

Fafaroma Francis ke cika shekaru 10 da fara jagorancin darikar Katolika

Shugaban mabiya darikar Katolika na duniya Fafaroma Francis yau litinin ya cika shekaru 10 a karagar mulki, inda ya ke jagorancin mabiyansa a sassa duniya. 

Fafaroma Francis na cika shekaru 10 da karbar jagorancin darikar Katolika na Duniya.
Fafaroma Francis na cika shekaru 10 da karbar jagorancin darikar Katolika na Duniya. AP - Alessandra Tarantino
Talla

A ranar 13 ga watan Maris na shekarar 2013 aka zabi Jorge Bergoglio domin maye gurbin Benedict na 16 wanda yayi murabus. 

Fafaroma Francis na ci gaba da taka rawa wajen tattauna batutuwa da dama da suka hada da abinda ya shafi matsalar bakin haure da gurbacewar muhalli da kuma zaman lafiya. 

Francis ya kuma ci gaba da mutunta matsayin darikar akan batutuwan da suka shafi zubar da ciki da kuma aure tsakanin masu jinsi guda. 

Fafaroman ya yi kokarin fadada zaman lafiya tsakanin mabiya darikar Katolika da kuma al’ummar musulmi wajen ganawa da Sheikh Ahmed al-Tayeb, babban limamin Masallachin Al-azhar da kuma ziyartar kasashe irinsu Jamhuriyar Dimokiradiyar Congo da Sudan ta Kudu domin ganawa da shugabannin su da nufin kawo karshen tashin hankalin da ake fama da shi a kasashen. 

Duk da yawan shekarunsa, Fafaroma Francis na ci gaba da tafiye tafiye zuwa kasashen duniya domin ganawa da mabiyansa. 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.