Isa ga babban shafi

Fafaroma ya kira da a kawo karshen zubar da jini a Sudan ta kudu

Fafaroma Francis a yau juma'a ya bukaci shugabannin Sudan ta Kudu da su yi  sabon tsalle don samar da zaman lafiya, a ranar farko ta ziyararsa zuwa kasa mafi karancin shekaru a duniya, wanda gwagwarmayar mulki da matsanancin talauci ya wargaza.

Fafaroma a kasar Sudan ta Kudu
Fafaroma a kasar Sudan ta Kudu REUTERS - YARA NARDI
Talla

Tsarin samar da zaman lafiya da sulhu yana buƙatar sadauki gargadin        Fafaroma yayin wani jawabi a gaban hukumomi a Juba babban birnin kasar Sudana ta kudu.

Daga shekarar 2013 zuwa 2018, wannan kasa mai mutane miliyan 12 tana fama da kazamin yakin basasa tsakanin magoya bayan shugabannin makiya biyu Salva Kiir da Riek Machar wanda ya yi sanadin mutuwar mutane 380,000 tare da raba miliyoyin mutane da gidajen su.

 Duk da yarjejeniyar zaman lafiya da aka kulla a shekarar 2018, ana ci gaba da tashe tashen hankula a wannan kasa.

Fafaroma mai shekaru 86 ya yi kashedi, tare da cewa al'ummomi masu zuwa za su girmama ko goge sunayen ku dangane da abin da kuke yi yanzu."

Ziyarar ta zaman lafiya  ita ce ziyarar Fafaroma ta farko a Sudan ta Kudu tun bayan da al'ummar da ke da rinjayen kiristoci suka sami 'yancin kai daga Sudan a shekara ta 2011.

A nasa bangaren, shugaba Salva Kiir ya sanar da janye dakatarwar da aka yanke a watan Nuwamba, na shiga tattaunawar zaman lafiya da gwamnatin kasar ta yi a birnin Roma na kasar Italiya da kungiyoyin 'yan tawaye. Tun a shekarar 2019 aka gudanar da wannan tattaunawa tsakanin gwamnati da kungiyoyin 'yan tawaye da dama da ba su rattaba hannu kan yarjejeniyar zaman lafiya ta 2018 ba.

Jim kadan da zuwan Fafaroman, dubban jama'a da ke daga tutoci, suka yi jerin gwano a kan tituna domin yi masa maraba da kade-kade.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.