Isa ga babban shafi

Sudan ta kudu ta kashe 'yan tawaye 50 a lardin Pibor mai fama da rikici

Rundunar sojin Sudan ta Kudu ta yi ikirarin hallaka ‘yan tawaye fiye da 50 bayan share tsawon kwanaki ana kokarin kakkabe ‘yan tawayen da suka kaddamar da farmaki a wasu lardunan kasar biyu. 

Sojin Sudan ta kudu.
Sojin Sudan ta kudu. REUTERS/James Akena
Talla

Kakakin rundunar sojin kasar Janar Lul Ruia Koang, ya ce za su ci gaba da farautar ‘yan tawayen har sai zuwa lokacin da aka dawo da doka da oda a larduna biyu wadanda matsalar ta shafa.   

Koang ya ce dubban ‘yan tawaye dauke da makamaki a lardin Jonglei ne suka mamaye yankin tare da cutar da al'ummar yankin saboda haka ba abin da ya dace face dakarun kasar su dauki matakin murkushesu. 

Kakakin rundunar Sojin ta Sudan ta kudu ya ce dakarun su sun yi artabu da 'yan tawayen a lardin Pibor kwatankwacin na lardin Jonglei yankunan da ke fama da hare-haren ‘yan tawayen musamman a Yirol da Akobo.

A cewarsa dakarun sun mayar da martani tare da baiwa al'umma kariya daga hare-haren 'yan ta'addan wadanda ke ikirarin tawaye a kasar mai fama da rikicin fiye da shekaru 10.

A jawabinsa gaban manema labarai Kakakin Sojin na Sudan ta kudu ya bayyana shirin yaye wasu dakarun Soji na musamman a yau juma'a wanda zai basu damar kara yawan Sojojin da kasar ke da su don baiwa jama'a cikakkiyar kariya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.