Isa ga babban shafi

Ba a taba ganin irin jana'izar fafaroma Benedict ba

Shugaban Darikar Katolika ta Duniya, Fafaroma Francis ya jagoranci jana’izar wanda ya gabace shi, wato fafaroma Benedict na 16 a dandalin St. Peter da ya samu halartar dubun-dubatan jama’a.

Mutane dubu 50 ne suka halarci jana'izar fafaroma Benedict na 16
Mutane dubu 50 ne suka halarci jana'izar fafaroma Benedict na 16 AFP - FILIPPO MONTEFORTE
Talla

An bayyana jana’izar a matsayin wadda ba a taba ganin makamanciyarta ba a zamani na baya-bayan nan, inda ta  samu halartar fitattun mutane da dubban malaman coci-coci daga sassan duniya domin yin ban-kwanar karshe ga tsohon fafaroman dan asalin Jamus.

Marigayin ya bai wa duniya mamaki a shekarar 2013, lokacin da ya yi murabus daga  kujerarsa ta shugaban Darikar Katolika, al’amarin da shi ne irinsa na farko cikin karni 6.

A karon farko kenan a tarihin zamanin baya-baya da wani fafaroma mai ci ya jagoranci jana’izar wanda ya gabace shi, yayin da ya gabatar da wa’azi a wurin jana’izar marigayin da ya mutu a ranar Asabar da ta gabata yana da shekaru 95.

A karshen addu’arsa, an ga yadda fafaroma Francis ya yi alamar gicciye kan akwatin gawar Benedict, sannan ya rissina masa kafin masu daukar akwatin gawar su yi gaba  da shi zuwa cikin majami’ar St. Peter.

Za a binne fafaroma Benedict a cikin kogon fadar Vatican da ke can kasan cocin St.Peter da ke zama hubbaren fafaroma-fafaroma da suka gabata.

Jami’an ‘yan sanda sun kiyasta cewa, akalla mutane dubu 50 ne suka halarci jana’izarsa a dandalin St.Peter a wannan Alhamis kuma tun da sanyin safiya suka yi dandazo duk da tsananin hunturu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.