Isa ga babban shafi

Hukumomin Iran sun bayar da belin Jafar Panahi

A kasar Iran an bayar da belin fitaccen darekta Jafar Panahi a yau Juma'a bayan ya tafi yajin cin abinci don nuna adawa da tsare shi na kusan watanni bakwai a kasa.

Jafar Panahi
Jafar Panahi © Réseaux sociaux
Talla

Jafar Panahi mai shekaru 62, wanda fina-finansa suka samu lambobin yabo a bukukuwan fina-finan Turai, an kama shi ne a ranar 11 ga watan Yuli kafin fara zanga-zanga a Iran a watan Satumba.

 Zai yi zaman gidan yari na shekaru shida da aka yanke masa a shekara ta 2010 saboda " farfaganda na adawa da tsarin ".

An sake shi "kwana biyu bayan ya tafi yajin cin abinci," in ji cibiyar kare hakkin bil'adama ta Iran (CHRI) da ke New York a shafin ta na Twitter.

Jaridar Shargh mai ra'ayin sauyi ta Iran ta tabbatar da sakinsa "bisa beli" tare da buga hoton dan fim din yana rungume da daya daga cikin magoya bayansa a lokacin da aka sako shi daga gidan yarin Evin da ke Tehran.

Matarsa ​​Tahereh Saeedi ta wallafa a shafin Instagram wani hoton da aka dauke shi daga gidan yari a cikin mota.

A wata sanarwa da mai dakinsa ta fitar a jiya alhamis, daraktan ya bayyana cewa ya fara yajin cin abinci a ranar 1 ga watan Fabrairu domin nuna rashin amincewa da sharuddan tsare shi.

Abin farin ciki ne da muka samu labarin sakin mai shirya fina-finai Jafar Panahi a yau. Ba mu manta da duk wadanda ke fama da tashin hankali da danniya  a Iran da duniya baki daya", Thierry Frémaux, babban wakilin kungiyar Cannes Film Festival, ya shaida wa AFP.

A ranar 15 ga watan Oktoba ne kotun kolin kasar Iran ta soke hukuncin da Panahi ya yanke a shekara ta 2010, tare da ba da umarnin sake gudanar da wani sabon shari'a, wanda hakan ya sa ake fatan za a sake shi nan take, amma ya ci gaba da zama a gidan yari.

Jafar Panahi ya lashe kyautar zinare a bikin fina-finai na Venise a shekarar 2000 a wani fim dinsa mai suna "Le Cercle". A cikin 2015, an ba shi lambar yabo ta Golden Bear a Balin don "Taxi Tehran" kuma, a cikin 2018, ya lashe kyautar mafi kyawun wasan kwaikwayo don "fuska uku" a bikin fina-finai na Cannes.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.