Isa ga babban shafi

Iran ta aiwatar da hukuncin kisa a kan sama da mutane 50 a wannan shekarar

Hukumar kare hakkin dan adam ta Human Rights ta ce mahukuntan Iran sun zartas da hukuncin kisa kan mutane 55 a cikin watan Janairun da muke ciki kadai, tare da tabbatar da irin tsoron da yanke hukuncin kisa da zartas da shi ke jefa jama’ar kasar.

Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce Iran ta aiwatar daa hukuncin kisa a kan mutaane sama da 50 a wannan shekarar kawai.
Kungiyoyin kare hakkin dan adam sun ce Iran ta aiwatar daa hukuncin kisa a kan mutaane sama da 50 a wannan shekarar kawai. © Humanists International
Talla

Wannan dai na zuwa ne bayan da kungiyar kare hakkin dan adam da Amnesty International ta ce abin takaici ne yadda kasar ta zartaswa wasu matasa masu shekarun da basu kai 25 ba hukuncin kisan, saboda kama su da laifin bada gudunmowa a zanga-zangar kasar ta nuna fushin kisan Mahsa Amini.

Human Righst Watch ta ce cikin mutane 55 din da aka zartaswa da hukuncin kisan, guda 37 an kama su ne da laifin ta’ammali da miyagun kwayoyi yayin da sauran aka zarge su da bada gudunmowa a zanga-zangar ta kisan Mahsa Amini.

Yanzu haka dai akwai sauran mutane 107 da ke gidajen yari da ke jiran a zartas musu da hukuncin na kisa, bayan da kotu ta yanke musu hukuncin saboda laifuka mabanbanta da aka kamasu da shi.

 

 

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.