Isa ga babban shafi

Iran ta sake zartas da hukuncin rataya a bainar jama'a

Iran ta zartar da hukuncin kisa ta hanyar rataya, kan mutum na biyu dangane da zanga-zangar da ta girgiza gwamnatin kasar kusan watanni uku, tare da bijirewa korafe-korafen da kasashen duniya suka yi kan hukuncin kisa kan wadanda ake zargi da shirya tarzomar.

Wasu mutane biyar da aka rataye a birnin Mashhad na kasar Iran kenan
Wasu mutane biyar da aka rataye a birnin Mashhad na kasar Iran kenan (Photo : AFP)
Talla

Wata kotu a birnin Mashhad ta yanke wa Majdreza Rahnavard mai shekaru 23 hukuncin kisa bisa samunsa da laifin kashe wasu jami’an tsaro biyu da wuka, tare da raunata wasu mutane hudu.

Rahotanni sun ce an rataye shi ne a bainar jama'a a cikin birnin, maimakon cikin gidan yari.

Kasashen Turai da Amurka sun mayar da martani da kakkausar murya bayan Iran a ranar Alhamis ta aiwatar da hukuncin kisa na farko da ke da alaka da zanga-zangar.

Mohsen Shekari, mai shekaru 23, an rataye shi ne bayan da aka yanke masa hukunci bisa laifin raunata wani jami’in tsaro.

Iran ta kira zanga-zangar da shirin haifar da tarzoma kuma ta ce abokan gaba na kasashen waje ne suka karfafa musu gwiwar aikata hakan.

Daraktan kungiyar kare hakkin bil'adama ta Iran da ke Oslo Mahmood Amiry-Moghaddam, ya ce an yanke wa Rahnavard hukuncin kisa ne bisa tilasta masa amsa laifin da bai aikata ba

An shafe makonni ana zanga-zangar ne sakamakon mutuwar Bakurdiya Mahsa Amini, mai shekaru 22, ‘yar kasar ta Iran da jami'an 'yan sanda suka kama bisa zargin keta ka'idojin shigar mata.

Zanga-zangar dai ita ce kalubale mafi girma ga gwamnatin tun bayan hambarar da gwamnatin Shah a shekarar 1979.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.