Isa ga babban shafi

Matashi dauke da bindiga ya kashe mutane a Brazil

A Brazil wani matashi dan shekara 16 sanye da alamar ‘yan Nazi dauke da bindiga ya kashe akalla mutane uku ciki har da wata karamar yarinya, tare da raunata wasu 11 a wasu makaratu biyu a jihar Espirito Santo da ke kudu maso gabashin kasar ta Brazil a jiya Juma’a.

Bindiga
Bindiga Reuters
Talla

Harin ya faru ne a Aracruz, wani birni mai mutane 100,000, mai tazarar kilomita 600 daga arewa maso gabashin Rio de Janeiro. Hukumomin kasar sun ce malamai uku da wani dalibi daga cikin wandada matashin ya raunata ba a bayyana sunayensu ba na cikin mawuyacin hali.

Maharin da ya rufe fuskarsa; ya shiga makarantar Primo Bitti, makarantar firamare da sakandare ta gwamnati da ya bari a watan Yuni, kamar yadda masu bincike suka bayyana.

Makaranta
Makaranta AFP - -

Bayan kutsawa cikin makarantar, sai ya shiga dakin ma’aikata ya bude wuta kan malamai da dama, inda ya kashe mutane biyu tare da raunata wasu tara, kamar yadda hukumomi suka ce.

Hotunan bidiyo da kafafen yada labarai suka fitar sun nuna yadda matashin ya shiga makarantar da bindiga a hannunsa, yayin da wasu da dama suka gudu.

Daga nan sai ya tafi, ba da nisa ba, zuwa Cibiyar Ilimi ta Praia de Coqueiral, wata makaranta mai zaman kanta, inda ya kashe wani matashi tare da raunata mutane biyu, kafin 'yan sanda su kama shi.

Hukumomin kasar sun kama maharin inji gwamnan jihar Espirito Santo, Renato Casagrande wanda ya ba da umarnin zaman makoki na kwanaki uku.

Kwamishinan ‘yan sandan farar hula Joao Francisco Filho ya shaida wa manema labarai cewa maharin “ba shi da takamaiman manufa” a lokacin da ya bude wuta, kuma ya sanar da shirya wannan harin tun shekaru biyu da suka gabata.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.