Isa ga babban shafi

Shugaba Jair Bolsonaro ya nemi afuwar yan kasar Brazil

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro ya nemi afuwar yan kasar da baki 'yan Venezuela a jiya talata bayan ziyarar da ya kai ga wasu matasa da ya nuna cewa karuwai,kalaman da suka  haifar da bacin rai.

Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro
Shugaban kasar Brazil Jair Bolsonaro REUTERS - ADRIANO MACHADO
Talla

Yan adawa musamman tsohon  shugaban kasar kuma dan takara na hannun dama Luiz Inacio Lula da Silva ya yi amfani da wannan dama inda ya nuna cewa Bolsonaro  da jimawa ya bayyana kiyamar sa ga baki.

A jawabinsa Bolsonaro ya bayyana cewa ‘’har Idan kalmominsa, da wasu suka  yi musu mummunar fassara ko kuma tare da haifar da rashin jin daɗi ga 'yan uwanmu mata na Venezuela, ina neman afuwa," in ji Bolsonaro a cikin wani faifan bidiyo da aka nuna ta yanar gizo.

Bolsonaro ya kara da cewa, "Alƙawarina a koda yaushe shine na yi maraba da taimaka wa duk mutanen da ke gujewa mulkin kama-karya a ko'ina a Duniya.

A cikin wannan bidiyon an hango Shugaba Bolsonaro, tare da matarsa ​​da wakilin madugun 'yan adawar Venezuela Juan Guaido.

Da jimawa Shugaba Bolsonaro ya amince da dan adawar Venezuela Juan Guaido a matsayin halastaccen shugaban Venezuela, maimakon shugaban gurguzu Nicolas Maduro.

Rosangela da Silva, matar Lula, ta wallafa wani bangare na wata hira da Bolsonaro a wata daya da ta gabata inda ya ce 'yan matan karuwai ne.

A watan Mayu, Bolsonaro shi ma ya ba da labarin yayin wani taron da aka watsa a gidan talabijin na jama'a.

Bolsonaro, wanda ya yi watsi da sukar ‘yan adawa, ya fada a cikin faifan bidiyo na ranar talata cewa, tsohuwar ministarsa ​​ta mata, Damares Alves, kusan nan da nan  ta binciki lamarin ‘yan matan kuma ya gano cewa a zahiri ba karuwai ba ne.

Shugaba Bolsonaro ya ce Alves da Uwargidan shugaban kasa Michelle Bolsonaro sun ziyarci 'yan matan ranar talata kuma  sun gano  cewa yan gudun hijirar Venezuelan.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.