Isa ga babban shafi

Turkiya za ta kammala gina gidaje 100.000 a Syria

Turkiyya ta lashi takobin kammala gina gidaje 100,000 a kasar Syria da yaki ya daidaita, labarin da ke zuwa a daidai lokacin da Ankara ke kokarin tanttance 'yan gudun hijirar Syria da suka tsere sama da shekaru 10 sabili da yaki.

Wani yanki da ke kan iyaka da kasar Turkiya
Wani yanki da ke kan iyaka da kasar Turkiya AP - Emrah Gurel
Talla

Ministan harakokin cikin gida na Turkiya Suleyman Soylu, wanda ke magana jiya Lahadi a ziyarar bude wasu gidaje 600 a yankin Idlib da ke hannun 'yan tawayen Syria, ya ce an gina gidaje 75,000 a cikin shekaru biyu da suka gabata.

"Ministan ya ce za su kammala gina gidaje 100,000  a karshen shekara. Shugaban kasar Turkiya Recep Tayyip Erdogan ya ce a cikin 'yan watannin nan yana son karfafa gwiwar 'yan gudun hijirar Syria miliyan daya daga cikin 'yan gudun hijirar kasar miliyan 3.7 da su koma gida ta hanyar gina musu gidaje da samar da ababen more rayuwa.

Gabanin zaben shugaban kasar Turkiya a shekara mai zuwa, kasancewar 'yan gudun hijira ya zama wani lamari mai sarkakiya a siyasance, musamman yadda Ankara ta fada cikin matsalar tattalin arziki.

Rikicin Syria ya fara ne a shekara ta 2011 tare da murkushe masu zanga-zangar lumana da gwamnatin kasar ta yi, kuma an tilasta wa miliyoyin mutane tserewa, yanzu haka a ciki da waje.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.