Isa ga babban shafi
Syria

Anyi amfani da sinadarin Chlorine kan 'yan tawayen Syria a 2016

Kungiyar dake yaki da amfani da makami mai guba a duniya tace, an yi amfani da sinadarin Chlorine a wani hari da aka kai wani yankin da ke hannun ‘yan tawayen  Syria a shekarar 2016, inda akalla mutane 20 suka fuskanci matsalar numfashi.

Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad
Shugaban kasar Syria Bashar al-Assad LOUAI BESHARA AFP
Talla

Cikin wani rahoton da kungiyar dake yaki da amfani makamai masu guba ta duniya OPCW, wanda ofishinta dake bincike kan hare-haren Syria ya gabatar, yace akwai dalilai masu ma'ana da za a hakikance cewa an yi amfani da sinadarin Chlorine na masana'antu a matsayin makami.

Rahotan na danganta hare-haren da ya auku kusa da wani asibiti da ke wajen garin Kafr Zeita wanda shaidun gani da ido suka bayyana cewa wani jirgin sama mai saukar ungulu ya jefa akalla wani abu guda a lokacin harin.

Silidar Sinadarin Chlorin da ake zargin anyi amfani da shi kan 'yan tawaye a rikicin Syria a shekarar 2016.
Silidar Sinadarin Chlorin da ake zargin anyi amfani da shi kan 'yan tawaye a rikicin Syria a shekarar 2016. AFP

Masu bincike sun tsinci wani silindar sinadarin chlorine na masana'antu da akayi amfani da shi adai-dai wurin da aka kai harin na ranar 1 ga watan Oktobar shekarar 2016, wanda kafofin sadarwa suka taimaka ta hujjoji da kuma shidun da sukayi hira da su.

An tabbatar da cewa lamarin ya shafi akalla mutane 20 da suka fuskaci matsalar nunfashi bayan harin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.