Isa ga babban shafi
Syria

Syria ke kan gaba wajen mutuwar mutane a dalilin bama-baman gefen hanya

Wani rahoto ya gano yadda Syria ke kan gaba a yawan mutanen da suka jikkata ko kuma rasa rayukansu sanadiyyar bama-baman da ake binnewa a gefen hanyoyi lokacin yaki, wanda ke nuna cewa kasar ta sha gaban Afghanistan, wadda a bara ta zama jagora wajen fama da matsalar.

Yadda yaki ya ragargaza yankin arewa maso yammacin kasar  Syria.
Yadda yaki ya ragargaza yankin arewa maso yammacin kasar Syria. AFP/File
Talla

Wani rahoton shekara shekara da hukumar kula da ababen fashewar karkashin kasa ta duniya kan fitar tun daga 1999 ya ce akalla mutane dubu 2 da 729 ne ko dai suka rasa ransu ko kuma suka jikkata sanadiyyar ababen fashewar na karkashin kasa a Syria.

Daga shekarar 2005 zuwa 2007 dai Colombia ke matsayin mafi yawan wadanda kan cutu daga ababen fashewar na karkashin kasa gabanin Afghanistan ta karbe jagoranci fiye da shekaru 14 a jere in banda bara da Syria ta shige gaba.

Rahoton hukumar na bana ya nuna yadda mutum dubu 2 da 492 suka mutu sakamakon taka ababen fashewar baya ga wasu mutum dubu 7 da 73 da suka jikkata cikin kasashe 54.

Alkaluman mutanen da suka cutu daga ababen fashewar na karkashin kasa acewar rahoton ya yi kasa da wanda aka gani a shekarar 2016 nan jumullar mutum dubu 9 da 440 ko da ya ke ya kuma dara alkaluman shekarar 2019 inda aka samu mutum dubu 5 da 853 wadanda ko dai suka jikkata ko kuma rasa rayukansu sanadiyyar ababen fashewar na karkashin kasa.

Rahoton ya ce har yanzu an gaza samun alkaluma kasa da mutum dubu 3 da 456 wanda aka samu a shekarar 2013 duk da yadda kasashe 164 suka shiga yarjejeniyar haramta dasa ababen fashewa a karkashin kasa tun shekarar 1997.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.