Isa ga babban shafi

Zanga-zangar nuna adawa ga hukumomin Iran a Faransa

Dubban jama'a ne suka fito a yau a birnin Paris da sauran garuruwan kasar Faransa domin nuna goyon bayansu ga zanga-zangar da ta girgiza Iran tun bayan mutuwar Mahsa Amini, tare da neman karin matsin lamba kan gwamnatin kasar ta Iran.

Wasu daga cikin maasu zanga zangar nuna adawa ga hukumomin Teheran a Faransa
Wasu daga cikin maasu zanga zangar nuna adawa ga hukumomin Teheran a Faransa AP - Christophe Gateau
Talla

A babban birnin kasar Faransa, mutane 2,500 ne suka halarci gangamin a cewar 'yan sanda. Masu zanga-zangar sun daga tutocin kasar Iran da dama da kwalaye da taken "Mata, Rayuwa, 'yanci" ko Suna kashe mu a cikin shuru.

A birnin Toulouse da ke kudu-maso-yammacin Faransa, dauke da tutocin Iran, wasu masu zanga-zangar 150 sun kafa sarkar dan Adam suna rera taken "Mata, Rayuwa, 'yanci", kuma a Lyon da ke , kusan mutane 250 suna rike da alamun goyon baya.

Saeed Shafiei, mai shekaru 47, ya shaidawa kamfanin dilancin labaren AFP cewa "suna son Faransa ta kara tunani kan 'yancin dan adam fiye da muradun tattalin arziki."

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.