Isa ga babban shafi

Hukumar kula da 'yan gudun Hijira ta Duniya na fuskantar karancin kudin kai agaji

Hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka game da yankewar kudaden tafiyar da ayyukan su mafi muni da aka taba, gani abin da ke zuwa lokacin da masu bayar da tallafin irin wadanan kudaden suka yi karanci.

Flippo Grandi, shugaban hukumar yan gudun hijira dake aiki da MDD
Flippo Grandi, shugaban hukumar yan gudun hijira dake aiki da MDD TONY KARUMBA / AFP
Talla

Shugaban hukumar Filippo Grandi, da ke wannan jawabi a wajen babban taron hukumar ta kula da ‘yan gudun hijira da aka saba gudanarwa ko wacce shekara ya ce abin fargaba ne matuka idan aka yi hasashen matsalar da ‘yan gudun hijira za su fada matukar wadannan kudi suka kammala yankewa. 

Filippo Grandi a wajen taron na birnin Geneva ya ce karewar kudaden na zuwa ne lokacin da kusan kowacce kasa ke fama da tashin hankali, yayin da adadin ‘yan gudun hijira ya zarta miliyan 100, adadi mafi yawa da aka taba gani a tarihi.

A cewar Grandi yakin Russia da Ukraine da ya tilastawa kusan mutane miliyan 5 barin gidajensu, abu ne da ya kara sama da dala biliyan 1 akan kasafin kudin hukumar na shekara, ya na mai cewa matukar hukumar bata sami dala miliyan 700 daga nan zuwa karshen wannan shekara ba, za’a samu mummunar matsalar da za ta tagayyara rayuwar ‘yan gudun hijira.

A don haka ne Mr Grandi ya yi kira da babbar murya ga hukumomi da manyan kasashen duniya da su waiwayi hukumar cikin gaggawa don bata tallafin kudade da nufin samun damar tafiyar da ayyukan ta.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.