Isa ga babban shafi

MDD ta mayar da 'yan gudun hijirar Congo 6,000 zuwa gida

Majalisar dinkin duniya ta ce ‘yan gudun hijirar Congo da suka tsere zuwa Zambia a shekarar 2017 akalla 6,000 sun koma gidajen su, tun bayan da ta kaddamar da wani shirin na musamman don mayar da mutanen gidajen su a shekarar da ta gabata.

'Yan gudun hijirar dai an mayar da su gida ne daga kasar Zambia
'Yan gudun hijirar dai an mayar da su gida ne daga kasar Zambia © rfi
Talla

Dubban mutane ne dai suka tsallaka zuwa Zambia daga kasar Congo shekaru biyar da suka gabata don tsira daga rikicin da ya barke tsakanin dakarun gwamnatin kasar da kungiyoyin masu rike da makamai da kuma rikicin kabilanci.

Duk da har yanzu wasu yankunan kasar ta tsakiyar Africa na fama da tsahin hankalin, amma dai yankin da mutane suka tsere a wancan lokacin na Haut-Katanga, ya samu cikakken tsaro karkashin shirin na hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniya.

Mutanen da aka mayar gidajen su mafi yawan su kananan yara sun zauna ne a sansanin ‘yan gudun hijira na Mantapala dake arewacin Zambia kuma an yi jigilar su ne cikin motocin Bas dan mayar da su gida Jamhuriyar dimokrdaiyyar Congo.

A cewar hukumar kula da ‘yan gudun hijira ta majalisar dinkin duniyar, nan da karshen shekara ana sanya ran mutane 11,000 cikin kusan miliyan guda da suka tserewa rikici a Congo su koma muhallan su na asali.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.