Isa ga babban shafi

Charles ya zama sarkin Ingila na 111

Yarima Charles ya maye gurbin Sarauniya Elizabeth ta II wadda ta rasu ta na da shekaru 96, inda yanzu haka ya zama Sarki Charlse na III.

Charles na III ya maye gurbin Elizabeth ta II.
Charles na III ya maye gurbin Elizabeth ta II. AP - Alastair Grant
Talla

An haifi Sarki Charles sarki na 111 ne a ranar 14 ga watan Nuwambar shekarar 1948, a fadar Buckingham inda aka rada masa suna Yarima Charlse Philip Arthur George na Edibura, ya kuma zama na biyu dake jiran gadon sarautar Ingila.

A ranar 15 ga watan Disambar shekarar 1948 aka yi limamin Kirista, ko kuma Archbisop na Kantabori ya masa batisma, yayin da kakansa kuma Sarki George na 6 ya rasu a ranar 6 ga watan Fabarairu na shekarar 1952, abinda ya baiwa mahaifiyar sa damar hawa karagar mulki, kana shi kuma ya zama Yarima mai jiran gado.

Anyi biki nada mahaifiyarsa Elizabeth a ranar 2 ga watan Yunin shekarar 1953, yayin da ya fara karatu a makarantar Gordonstoun a arewa maso gabashin Scotland, inda mahaifinsa Yarima Philip yayi karatu.

Sarki Chales na 111 yayi aikin sojan ruwa a shekarar 1971, kamar yadda mahaifinsa yayi, a shekarar 10974 kuma yayi aiki da jiragen saman yakin kasar.

A 1976 ya zama kwamandan sojin ruwan Birtaniya..

Ya auri Diana wadda ta haifa masa yaya biyu wato Yariam William da Yarima Harry, kafin su rabu ta kuma rasu a hadarin mota, kama ya auri tsohuwar budurwarsa Camilia.

Yarima Charles ya zama Sarki Charles na 111 sakamakon rasuwar mahaifiyarsa a wannan alhamis din, yana da shekaru 73.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.