Isa ga babban shafi

Mataimakiyar Shugaban Argentina ta tsallake rijiya da baya

Cristina Kirchner mataimakiyar shugaban kasar Argentina, mai shekaru 69, ta tsira daga harin da aka kai mata dab da gidanta na Buenos Aires a jiya Alhamis bayan da Fernando Andre Sabag Montiel mutumin da ake tsare da shi mai shekaru 35, dan kasar Brazil dauke da bindiga ya nemi hallaka ta kai tsaye .

Wani mutum yana nuna bindiga kai tsaye ga Kirchner
Wani mutum yana nuna bindiga kai tsaye ga Kirchner AFP - HANDOUT
Talla

Sakonnin kaduwa da nuna goyon baya na zuwa daga sassa daban-daban na duniya a yau Juma’a bayan da Fernando Andre Sabag Montiel ya yi kokarin harbin mataimakiyar shugaban kasar Argentina Cristina Kirchner a filin wasa, sai dai bindigar ta kasa tashi.

Lamarin ya faru ne a unguwar Recoleta da ke birnin Buenos Aires inda magoya bayanta ke taruwa a kowane dare tun daga ranar 22 ga watan Agusta, lokacin da masu gabatar da kara na Argentina suka sanar da cewa za su nemi hukuncin daurin shekaru 12 a kan Kirchner a shari'ar da ake yi na cin hanci da rashawa, da kuma haramta mata shiga harkokin siyasa.

‘Yan sanda na gudanar da bincike kan ko maharin da aka kama a wurin, na gano cewa ko maharin ya samu goyon baya daga wani ko wata kungiya daban wajen kitsa wannan hari.

Nan take aka kuma tuhume shi da kokarin aikata kisan gilla.

A baya dai an kama shi da laifin mallakar makamai ba bisa ka'ida ba, kamar yadda majiyar 'yan sanda ta ruwaito daga kamfanin dillancin labarai na Telam.

Hotunan da suka fito daga shafukan sada zumunta sun nuna mutumin yana wasa da tattoo na Nazi, kuma 'yan sanda sun shaida wa manema labarai cewa sun gano harsashi 100 a wani gida da ya yi haya a wajen birnin Buenos Aires.

Hotunan lamarin sun nuna wani mutum yana nuna bindiga kai tsaye ga Kirchner, macen da ta  kasance shugabar kasa daga 2007 zuwa 2015 kuma tana fuskantar tuhumar cin hanci da rashawa tun daga wancan lokacin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.