NATO ta ce ba ta da wani shirin kafa sansani a kasashen Sweden ko Finland
Kungiyar tsaro ta NATO ta fara bin matakan shigar da kasashen Sweden da Finland cikinta, a wani yunkuri na kara fadada ayyukanta na soji zuwa kasashe 32.
Wallafawa ranar:
Wannan dai na daga cikin matakan da kungiyar ta dauka da nufin mayar da martani kan mamayar da kasar Rasha ta yi wa makwabciyarta wato Ukraine a ranar 24 ga watan Fabrairu.
Shugaban kungiyar Jens Stoltenberg bayan sanya hannu kan was muhimman takarardu da za su sharewa kaashen fagen shiga NATO, ya bayyana al’amarin a matsayin tarihi da ba za a mance da shi ba.
Sai dai NATO ta ce a halin yanzu ba ta da wani shiri na aika dakaru zuwa kasashen Sweden da Finland da zarar sun kasance mambobinta.
A watan Mayun 2022 ne dai kasashen suka nuna sha’awar su ta shiga kungiyar tsaro ta NATO, bayan da Rasha ta kaddamar da mamayar ta a Ukraine a cikin watan Fabrairu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu