Isa ga babban shafi
WHO-Coronavirus

WHO ta roki mawadatan kasashe su taimaka da dala biliyan 16 don yakar covid-19

Hukumar Lafiya ta Duniya ta WHO ta roki ma’azurtan kasashe su sauke nauyin da ke kansu wajen taimakawa da kudaden da aka alkawarta na dala biliyan 16 don yaki da cutar covid-19.

Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus.
Shugaban hukumar Lafiya ta Duniya Tedros Adhanom Ghebreyesus. REUTERS - DENIS BALIBOUSE
Talla

Acewar hukumar ta WHO kudaden dala biliyan 16 da ake dakonsu daga ma’azurtan kasashe za su taimaka wajen yiwa matsalar covid-19 da ta addabi duniya kwab daya matukar aka iya samar da su a shekarar nan.

Karkashin shirin ACT-A da ke kunshe da shirin covax akwai yunkurin magance kalubalen lafiyar da annobar ta covid-19 ta haifarwa duniya ciki har da wadata duniya da rigakafin cutar, kana kayakin gwaji da na jinyar cutar baya ga kayakin bayar da kariya.

WHO ta bayyana cewa shirin na ACT-A da ya bukaci tsabar kudi dala biliyan 23 da rabi don tafiyar da harkokin da aka tsara daga watan Oktoban 2021 zuwa Satumban 2022, har zuwa yanzu dala miliyan 800 aka iya samarwa.

Hukumar ta ce yanzu haka shirin na bukatar dala biliyan 16 daga mawadatan kasashen ne don cike gibin da aka samu a kokarin yakar cutar, inda shugaban WHO Tedros Adhanom Ghebreyesus ke cewa yaduwar nau’in corona na delta ya tsananta bukatar da ake da ita ta wadata duniya da kayakin yaki da cutar da kuma na kariya.

Acewar Dr Ghebreyesus kimiyya ta bayar da damar iya yakar annobar ta covid-19 tare da kawar da ita daga ban kasa matukar kowanne bangare zai sadaukar musamman mawadata da ke da karfin tattalin arziki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.