Isa ga babban shafi
Corona-WHO

Duniya na neman allurar hana kamuwa da corona ne ba rigakafi ba- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya ta yi gargadi kan matakin maimatawa wadanda suka karbi rigakafin corona karin wasu alluran rigakafin cutar na daban a kokarin dakile harbuwa da sabbin nau’in cutar da ke sake bayyana, dai dai lokacin da nau’in Omicron ke ci gaba da yaduwa a sassan Duniya.

Nau'in corona na Omicron na cikin wadanda suka tayar da hankalin duniya saboda saurin yaduwarsa zuwa kasashe fiye da 140 a kankanin lokaci.
Nau'in corona na Omicron na cikin wadanda suka tayar da hankalin duniya saboda saurin yaduwarsa zuwa kasashe fiye da 140 a kankanin lokaci. Justin TALLIS AFP/File
Talla

A gargadin da kwararru na hukumar ta WHO suka fitar kan shirin sake yiwa mutanen da suka karbi alluran rigakafin akalla biyu ko 3 karin wasu allurai, sun ce bukatar da ake da ita a yanzu shi ne samar da alluran da za su bayar da kariya daga harbuwa da cutar maimakon kara bai wa mutanen da tun tuni sun karbi rigakafin karin wani rigakafi na daban.

Tawagar kwararrun da ke nazari kan alluran rigakafin da zuwa yanzu kamfanonin samar da magunguna na Duniya suka yi, sun ce maimakon mayar da hankali wajen samar da rigakafin kowanne nau’I na corona da ya bulla, bukatar da ke da akwai shi ne samar da allura guda daya kwakkwara da za ta hana harbuwa da cutar ko da anyi cudanya da masu ita.

Sanarwar da kwararrun na WHO suka fitar ta ce la’akari da yadda nau’in Omicron ya yi saurin bazuwa kasashe 149 a kankanin lokaci hakan na nuna matakan da ake dauka kama daga yaki da cutar da kuma dakile yaduwarta ta hanyar rigakafin da ake yiwa jama'a basu amfanar kamar yadda ake tsammani ba.

Kwararrun na hukumar Lafiya ta Duniya, sun tsaya kan cewa bukatar da Duniya ke da shi a yanzu bai wuce kamfanonin magunguna su samar da wata allura guda ba, wadda ko dai za ta hana mutane harbuwa da cutar ko kuma ta hana wadanda suka harbu kwantawa rashin lafiya ko ma ta hana mutuwa baki daya.

Zuwa yanzu kasashe da dama ne suka daura damarar sake yiwa al'ummominsu allurar rigakafin a karo na 3 don dakile yaduwar nau'in Omicron da ya fi kowanne nau'i saurin yaduwa tun bayan bullar cutar a cikin watan Disamban 2019.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.