Isa ga babban shafi
Turai-WHO

Rabin al'ummar Turai za su harbu da Omicron cikin makwanni 6 zuwa 8- WHO

Hukumar Lafiya ta Duniya WHO ta yi gargadin cewa rabin al’ummar Turai za su harbu da nau’in corona na Omicron nan da makwanni 6 zuwa 8 masu zuwa.

Hans Kluge, shugaban WHO shiyyar Turai.
Hans Kluge, shugaban WHO shiyyar Turai. © AP
Talla

Shugaban WHO shiyyar Turai Dr Hans Kluge ya ce tsanantar nau’in cutar na Omicron ya kai kololuwa fiye da yadda nahiyar ta gani a lokacin nau’in Delta musamman a makon farko na shekarar 2022 da ta gama fantsama ilahirin kasashen Turai.

Acewar Dr Kluge Turai ta samu sabbin harbuwa da corona miliyan 7 a makon farko na 2022 fiye da ninki biyu na adadin mutanen da kan harbu cikin mako biyu lokacin tsanantar Delta.

A jawabinsa yayin taron manema labarai Dr Kluge ya ce nau’in cutar na Omicron ya sake jefa Turai cikin halin tsaka mai wuya fiye da halin da nahiyar ta shiga lokacin bullar Delta.

Dr Kluge cikin jawabin nasa ya bayyana yadda hasashen babbar cibiyar kiwon lafiya ta Turai ke sanar da yiwuwar kashi 50 cikin 100 na al’ummar kassahen su harbu da corona nan da ‘yan makwanni masu zuwa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.