Isa ga babban shafi
Amurka-Gobara

Gobara ta kashe tarin kananan yara a birnin Philadelphia na Amurka

Mutane goma sha uku ne ciki har da kananan yara bakwai suka mutu sakamakon tashin wata gobara a wani ginin bene mai hawa uku a birnin Philadelphia da ke gabashin Amurka.

Yankin da aka samu gobara a jihar Philadelphia ta Amurka.
Yankin da aka samu gobara a jihar Philadelphia ta Amurka. Ed JONES AFP
Talla

Mataimakin kwamishinan ma’aikatar kashe gobara ta Philadelphia Craig Murphy ya ce adadin ya yi tsara sosai, tare da cewa wannan ce gobara mafi muni da ya taba gani cikin shekaru 35 yana aiki.

Ma'aikatar kashe gobara ta birnin ta ce jami'anta sun isa wurin da lamarin ya faru a unguwar Fairmount da karfe 6:40 na safe, kuma kafin a shawo kanta sau da jami’ai suka dauki tsawon minti hamsin.

Magajin garin Philadelphia, Jim Kenney, ya ce gidan wanda gobarar ta auku a hawa na biyu, mallakar Hukumar Gidajen Philadelphia ne.

Ya ce wannan ba shakka yana daya daga cikin mafi munin ranaku a tarihin garin wajen asarar mutane da dama a irin wannan ibtila’i.

Jaridar Philadelphia Inquirer ta ruwaito 'yan sanda na cewa an mayar da gidan mai hawa uku zuwa gidaje biyu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.