Isa ga babban shafi
Amurka - Gobarar Daji

Gobarar daji ta kone daruruwan gidaje a Colorado

Daruruwan gidajen al’umma sun kone kurmus sakamakon wata maahaukaciyar wutar daji mai gudun gaske wadda afka wa jihar Colorado ta Amurka kamar yadda hukumomin kasar suka bayyana.

Yadda gobarar daji ta rika kone gine-gine a jihar Colorado da ke kasar Amurka
Yadda gobarar daji ta rika kone gine-gine a jihar Colorado da ke kasar Amurka AFP - JASON CONNOLLY
Talla

Wutar ta cinye kadada akalla dubu 1 da 600 a gundumar Boulder, inda kuma aka bada gargadin cewa, da yiwuwar a samu asarar rayuka da raunuka ganin yadda wutar dajin ta doshi gidajen otel-otel da manyan kantuna a garin Superior.

Tuni jaridar Colorado Sun ta rawaito cewa, an kwantar da wasu mutane a asibiti saboda rauni na kuna a jikinsu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.