Isa ga babban shafi
Algeria

Gobarar daji ta lakume rayukan mutane fiye da 70 a Algeria

Jami’an tsaro a kasar Algeria sun sake kama karin mutane 22 wadanda ake zarginsu da hannu wajen haddasa tashin gobarar dajin da ta lakume rayukan mutane sama da 70.

Wani mutum yayin kallon Gobarar daji a kusa da kauyen Larbaa a yankin Kabyle mai tsaunuka, mai nisan kilomita 100 daga Algiers babban birnin Algeria. 11 ga watan Agusta, 2021.
Wani mutum yayin kallon Gobarar daji a kusa da kauyen Larbaa a yankin Kabyle mai tsaunuka, mai nisan kilomita 100 daga Algiers babban birnin Algeria. 11 ga watan Agusta, 2021. AP - Fateh Guidoum
Talla

Wannan ce dai gobarar daji mafi muni a tarihin kasar, kasancewar ta lalata dubban filayen noma tare da halaka namun daji baya ga mutanen da suka rasu sanadiyyar tashin ta a sassan kasar sama da 70.

Rahotanni sun bayyana cewa cikin mutanen da suka mutu, 28 sojoji ne da ke aikin taimakawa jami’an kashe gobara wajen ceto mutanen da wutar dajin ta rutsa da su.

Har yanzu dai ma'aikatan kashe gobara da ke samun goyan bayan injiniyoyin sojoji da masu sa kai na farar hula suna ci gaba da fafutukar kashe gobarar dajin da ta tashi a yankuna 35 da ke cikin larduna 12 na arewacin kasar ta Algeria, sai dai sun samu nasarar kashe wutar da ta fi muni a lardin Tizi Ouzou a cewar hukumar agajin gaggawa ta kasar.

Zuwa yanzu akalla mutane 71 suka mutu tun daga ranar Litinin bayan tashin gobarar dajin.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.