Gobarar dajin California ta kone fadin kasar da ya zarce girman Los Angeles
Gobarar dajin da masana suka yiwa lakabi da Dixie na ci gaba da yin karfi a arewacin California da ke Amurka, abin da ya sa wutar zama ta biyu mafi muni a tarihin jihar.
Wallafawa ranar:
Zuwa safiyar ranar Lahadi gobarar dajin ta kone fadin kasar da ya kai kadada dubu 463 da 477 fiye da kadada dubu 447 da 723 da ta kone tun a ranar Asabar.
Kawo yanzu fadin kasar wutar dajin ta lakume ya zarce girman birnin Los Angeles.
Jami’an kwana-kwana fiye da dubu 5 ke kokarin kashe gobarar dajin ta Dixie, da ta yi sanadin bacewar mutane akalla 5.
Masana dai sun yi hasashen cewa wutar da ta tashi tun a ranar 13 ga watan Yuli, za ta iya zarce ranar 20 ga watan Agustan nan kafin kawo karshenta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu