Isa ga babban shafi
Turkiya-Gobarar daji

Gobarar daji ta addabi kudancin nahiyar Turai

Al’ummomin gwamman kauyuka ne aka kwashe a yankunan yawon bude ido da ke kudancin Turkiyya a jiya Lahadi, inda gobarar dajin da ta lakume rayukan mutane 6 ke ci gaba da ci a kwana na 5 a jere, a yayin da kasashen Girka, Spain da Italiya suka samu na su rabon na  wutar dajin.

Gobarar daji a Australia.
Gobarar daji a Australia. JOSH EDELSON AFP/File
Talla

Gobarar da ta tashi sakamakon yanayi na tsananin zafi gami da iska mai karfin gaske har ma da sauyin yanayi ta fi yin barna idan aka kwatanta da na lokutan baya a cewar alkalumman da aka samu daga Tarayyar Turai.

Turkiyya na fuskantar irin wannan  gobara mafi muni a cikin shekaru 10 da suka gabata, inda kusan hecta dubu 95 na daji ta salwanta a cikin wannan shekarar, akasin dubu 13 da 516 a tsakanin shekarar 2008 zuwa 2020.

Rahotanni sun ce an kwashe al’ummar wani yanki da ke makwaftaka da garin Bodrum da ke jan hankalin masu yawon bude ido, a yayin da iska mai karfi daga gundumar Milas ke ta’azzara wutar.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.