Isa ga babban shafi
Cyprus - Iftila'i

Tsananin zafi ya haifar da gobarar daji mafi muni a Cyprus

Daruruwan jami’an kwana kwana sun dukufa wajen kokarin kashe mummunar gobarar dajin da ta tilastawa dubban mutane tsrewa daga kauyukansu a kasar Cyprus, wadda kawo yanzu ta kasha mutane 4 tare da lalata dubban gidaje a yankin Arakapas.

Ma'aikatan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar daji a kasar Cyprus 04-07-21
Ma'aikatan kwana-kwana na kokarin kashe gobarar daji a kasar Cyprus 04-07-21 - AFP
Talla

Gobrar dajin da ta tashi tun a ranar Asabar daga yankin tsaunukan Troodos sakamakon tsananin zafi, ta lalata gonakin da fadinsu ya zarce murabba’in kilomita 50.

Tuni dai kasashen Girka, Isra’ila da wasu karin kasashe suka aike da jirage masu saukar ungulu domin taimakawa jami’an kwana kwanan wajen kashe gobarar dajin mafi muni da aka gani a kasar ta Cyprus tun shekarar 1974.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.