Isa ga babban shafi
KARANCIN ABINCI

Gurbacewar muhalli na barazar haifar da mummunar fari a shekaru masu zuwa - FAO

Wani rahoto da hukumar abinci ta duniya ta fitar ya nuna cewa, karancin fadin kasa da kuma ruwa ya haifar da barazanar fuskantar mummunan fari ga al’ummar da ke tafe, wanda ake hasashen zai shafi muhalli ma da sha’anin tsaro.

Hamadar Mauritania
Hamadar Mauritania ( Photo : AFP )
Talla

Rahoton wanda ya mayar da hankali kan yanayin karancin kasa da albarkatun ruwa da kuma yadda za a habaka hanyoyin samar da abinci ya nuna cewa mutane da dama na cikin damuwa, yayin da ake ta fafutukar yadda za a ciyar da al'ummar duniya da ake sa ran za su karu da sama da kashi daya bisa hudu cikin shekaru talatin masu zuwa.

Hukumar ta yi kiyasin cewa a halin da ake ciki yanzu bangaren noma zai bukaci karin kashi 35 cikin 100 na ruwa don samar da karin abincin da ake bukata a cikin shekaru masu zuwa.

Hukumar ta Majalisar Dinkin Duniya ta ce matsawar aka gaza daukar matakai, hakan zai iya haifar da bala'o'i na muhalli, da da albarkatun kasa, da kuma haifar da sabbin kalubale da rikice-rikice na zamantakewa a tsakanin al’ummar duniya.

Babban daraktan hukumar, Qu Dongyu, ya ce abincin da ake nomawa a halin yanzu ba ya isa, bare a samu wanda za a ajiye domin shirin ko ta kwana,.

Ko da yake ya ce duk da wadannan kalubale, tsarin noma na iya taka muhimmiyar rawa wajen kawar da wadannan matsalolin da kuma bayar da gudummawa mai kyau ga yanayi da manufofin raya kasa,.

Hukumar ta ce, za a bukaci hanzarta bunkasa fasahar kere-kere domin bunkasa yadda ake gudanar da ayyukan noma da kuma dora amfani da albarkatu a kan turba mai dorewa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.