Isa ga babban shafi
Afrika-Abinci

Mutane miliyan 23 za su fuskanci matsalar karancin Abinci a Afrika- rahoto

Cibiyar da ke da kula da abinci ta nahiyar Afrika ta ce matsalar karancin abinci na ci gaba da girmama a yankin Sahel, da kasashen yankin yammacin Afrika, inda yanzu haka kimanin mutane miliyan 23 da dubu 700 kwatankwacin kashi 7.4 na al’ummar kasashe 15 da aka nazarta ke cikin matsalar.

Tun kafin yanzu hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya ta yi hasashen fuskantar tsananin yunwa mafi muni a nahiyar Afrika.
Tun kafin yanzu hukumar abinci ta majalisar dinkin duniya ta yi hasashen fuskantar tsananin yunwa mafi muni a nahiyar Afrika. 路透社
Talla

Wannan adadi dai na iya karuwa a wannan lokaci na tsakanin rani da damina kamar yadda alkaluman cibiyar suka nuna cikin wani rahoton karshen shekara da ta fitar.

Kimanin mutane miliyan 33 da dubu dari 4 ne za su iya fadawa cikin matsananciyar barazanar karancin abinci idan har ba a dauki wasu matakai na gaggawa ba, a cewar wata kwararriya daga cibiyar wadda ke taronta ta hoton bidiyo.

Jami'ar ta ce adadin na wakiltar kashi 10.5 na al’ummomin kasashen.

Laurent Bossard babban daraktan cibiyar hadakar kasashen sahel da na yammacin afrika (CSAO), ya ce babban dalilin faruwar matsalar karancin abincin ita ce, rashin tsaro da tashe tashen hankulla da yankin ke fama da shi 

Inda ake da fagagen daga guda 2 daya na  cikin yankin da ya hada iyakokin 3 da suka hada kasshen  Mali, Burkina Faso da Niger, inda ake kai munanna hare haren ta’addanci dake haifar da hasarar rayuka masu yawa daga mayakan kungiyoyin yan ta’addan Al-Qaïda (ISIS).

Fagen daga  na biyu kuma shi ne wanda ya hada yankunan kasashen yankin tafkin Tchadi Najeriya Nijer Tchadi da kuma Kamaru, yankin da ya kasance  maboyar kungiyar Boko Haram da ballalinta, da kuma kumgiyar Iswap dake biyayya ga kungiyar ISIS.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.