Isa ga babban shafi
Abinci-FAO

Duniya na fuskantar tsadar abinci mafi muni cikin shekaru 10- FAO

Hukumar abinci ta Majalisar Dinkin Duniya ta koka da yadda tashin farashin kayan abincin ke kokarin ninka yawan yunwar da ta yi hasashen za a gani cikin shekarar nan.

Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya.
Wata kasuwar saida kayayyakin abinci a birnin Legas dake kudancin Najeriya. AP - Sunday Alamba
Talla

Alkaluman da hukumar ta fitar ya nuna cewa, farashin kayan abincin a baya-bayan na tashi cikin sauri a kusan dukkan sassan Duniya, cikin wani yanayi da ba a taba gani ba a shekaru 10 da suka gabata.

A cewar hukumar ta FAO annobar covid-19 ta taimaka matuka wajen kara karanci da kuma tsadar abinci a sassan Duniya da akalla kashi 40 wanda ke matsayin tashi mafi tsanani da aka gani tun bayan shekarar 2011.

Shugaban sashen tattalin arziki na FAO Arif Husain ya ce farashin masara ya karu da kashi 88 yayinda waken suya ya karu da kashi 73 kana kayan abinci nau’ikan hatsi da mayukan girki ya karu da kashi 38 kana sukari da kashi 34 sai nama da kashi 10, alkaluman da jami’in ke cewa barazana ce ga tattalin arzikin Duniya.

Bayanai na nuna tashin farashin kayan da irin wanda aka gani a shekarar 2007 zuwa 2008 da kuma shekarar 2010 zuwa 2011 lokacin da kasashen Larabawa suka yi boren sauyin gwamnati da ya haddasa rikici tare da karancin abinci a yankuna daban-daban an Duniya.

Hukumar ta ce duk lokacin girbi zai bayar da damar sassautowar farashin kayakin, amma alamun na nuna abu ne mai wuya farashin ya dawo kamar baya a cikin sauki, la’akari da yadda annobar covid-19 ta shafi tattalin arzikin kasashe tare da takaita harkokin noma a yankuna da dama.

Haka zalika, hukumar ta FAO ta ce matsalar dumamar yanayi ta taimakawa wajen haddasa karancin abinci sakamakon fuskantar ambaliyar ruwa ko kuma jinkirin faduwar damuna a yankunan da suka dogara da ruwan sama wajen noma.

Hukumar ta FAO ta ce Lebanon ce kan gaba a jerin kasashen da za su fuskanci ko kuma su ket saka da fuskantar matsalar ta karancin abinci inda farashin kayaki suka ninka zuwa kasha 226.

Sauran kasashen sun hada da Argentina, da Najeriya inda cikin kankanin lokaci mutane miliyan 7 suka fada cikin talauci tukuna daidakun kasashen Afrika da Asiya da kuma latin Amurka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.