Isa ga babban shafi
Sauyin yanayi

Kananan yara na zanga-zanga kan dumamar yanayi a birnin Glasgow

Dubban kananan yara a birnin Glasgow na Scotland sun gudanar da zanga-zangar kalubalantar yadda shugabannin da suka halarci taron yanayi na COP26 suka gaza daukar matakan da suka dace a yaki da dumamar yanayi.

Kananan yaran da ke zanga-zangar kalubalantar matakan yaki da dumamar yanayi a Glasgow bisa jagorancin Greta Thunberg.
Kananan yaran da ke zanga-zangar kalubalantar matakan yaki da dumamar yanayi a Glasgow bisa jagorancin Greta Thunberg. © AP - Andrew Milligan
Talla

Dubban matasan da suka shirya zanga-zangar ta kwanaki biyu na da nufin janyo hankalin shugabanni musamman na kasashen da ke fitar da kaso mai yawa na na sinadarin hayakin Carbon mai gurbata muhalli don ragewa da nufin tunkarar matsalar ta dumamar yanayi da ke barazana ga duniya baki daya.

Zanga-zangar matasan wadda aka tsara za ta gudana har a juma'a mai zuwa nisa jagorancin manyan masu fafatukar yaki da matsalar ta dumamar yanayi a matakin yara wato Greta Thunberg da Vaessa Nakate.

Zanga-zangar ta mayar da hankali kan bukatar rage yawan tiriri mai gurbata muhalli da kuma kira wajen daukar matakan gaggawa wajen ceto duniya daga barazanar da ta ke fuskanta.

An dai faro gangamin daga tsakar birnin na Glasgow inda yaran suka rike kwalaye masu dauke da rubuce-rubuce daban-daban dukkanninsu dauke da kiraye-kirayen ganin an dauki matakin yaki da dumamar yanayin.

Guda cikin masu zanga-zangar Zara ‘yar shekaru 9 da ke rike da allo mai dauke da rubutun ‘‘babu Duniya ta biyu’’ tare da fadin idan ba a dauki mataki yanzu ba sai yaushe? ta shaidawa manema labarai cewa suna da fatan zanga-zangar ta taimaka wajen daukar matakan magance matsalar.

Zara wadda ta halarci zanga-zangar bisa rakiyar mahaifiyarta, ta ce akwai bukatar shuka miliyoyin bishiyu a sassan daban-daban na duniya haka zalika samar da karin dabbobi wanda kuma nauyi ne da ke kan kowanne dan adam.

Ita kuwa Beth Donaldson cewa ya yi matasa da kananan yara sun kosa da irin alkawurran da shugabannin ke yi babu cika dangane da matsalar ta dumamar yanayi.

 Wakilan kananan yara daga mabanbantan kasashe akalla 200 suka halarci zanga-zangar wadanda ke kokarin ganin mahukunta sun mutunta yarjejeniyar yanayi ta Paris don ceto duniya.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.