Isa ga babban shafi
SIYASAR-AMURKA

Trump ya kirkiro dandalin sada zumunta na kan sa

Tsohon Shugaban Amurka Donald Trump ya bayyana shirin kaddamar da dandalin sada zumunta a intanet na kashin kan sa da zummar ganin ya samu damar aikewa da sakonnin sa bayan da kamfanonin twitter da Facebook suka dakatar da shi, sakamakon harin da magoya bayan sa suka kai majalisar dokokin Amurka.

Donald Trump da sabuwar manhajar sa ta "Truth social"
Donald Trump da sabuwar manhajar sa ta "Truth social" Chris DELMAS AFP
Talla

Tsohon shugaban yace kamfanin yada labaran sa na TMTG ne zai mallaki dandalin wanda ya yiwa suna ‘TRUTH Social’, kuma ana saran ya fara aikin karbar baki daga watan gobe, yayin da ake iya samun manhajar sa a intanet domin amfani da shi.

Trump yace ya kirkiro dandalin ’TRUTH Social da TMTG’ domin kalubalantar kama karyar da yace manyan kamfanonin sadarwar duniya irin su Facebook da twitter ke yi.

Trump yace kamfanin sa zai mallaki "TRUTH Social"
Trump yace kamfanin sa zai mallaki "TRUTH Social" Chris DELMAS AFP

Tsohon shugaban ya bayyana cewar, yayin da kungiyar Taliban ke amfani da twitter sosai, sai ga shi an hana shugaban Amurka mafi farin jini, inda yake cewa ba zasu amince da haka ba.

Trump ya dade yana sukar kamfanonin sada zumuntar saboda matakan da suke dauka akan sa na yada labaran karya wadanda suka ce ya sabawa dokokin su.

Daukar matakin dakatar da tsohon shugaban ya harzuka shi, musamman lokacin da yake ta bada labaran cewar shine ya samu nasarar zaben shugaban kasar da akayi a Amurka bara, bayan hukumar zabe da majalisar dokoki sun tabbatar da cewar ya sha kaye.

Wannan matsayi na sa ya sa magoya bayan sa kai hari majalisar dokokin, abinda yayi sanadiyar rasa rayuka.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.